Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce nahiyar Afirka ta rabu da cutar polio bayan kwashe shekaru da dama ana yaki da ita ta hanyar allurar rigakafi a kasashen duniya da dama.

Wacce ta jagoranci binciken Farfesa Rose Gana Fomban Leke ta ce babu wanda ke dauke da cutar inda ta bayyana yau a matsayin rana mai dimbin tarihi ga Afirka.

Wannan dai ke nuna cewa Afirka tayi nasarar kawar da cutar polio daga nahiyar.

Tun daga shekarar 1996 Hukumar Lafiya ta fara yaki da cutar polio wajen yiwa yara rigakafi wanda matakin ya kare yara miliyan guda da dubu 800 daga zama guragu da kuma kare rayukan mutane 180,000.

Hukumar ta ce a cikin shekaru 30 da suka gabata, an kashe akalla Dala biliyan 19 wajen yaki da cutar, yayin da yanzu banda kasashen Afghanistan da Pakistan babu wata kasa dake dauke da cutar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ma’aikata sama da 20 suka rasa rayukan su wajen aikin yaki da cutar, saboda haka wannan gagarumar nasara ce aka samu wajen ganin bayan ta a Afirka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *