Kwamitin fadar shugaban kasa da ke binciken dakataccen shugaban hukumar EFCC ya bada shawarar a sallami Ibrahim Magu.

Kwamitin, a karkashin jagorancin tsohon Alkalin kotun daukaka kara Ayo Isah Salami, ya ba Buhari jerin shawarin da ya yi, kuma daga ciki akwai bukatar hukunta Magu bisa zargin rashawa da ci da kujerar sa.

An dai zargi Magu da saba dokar hukumar kula da da’ar ma’aikata, ta hanyar kin bayyana wasu dukiyoyin da ya mallaka lokacin da ya shiga ofis a shekara ta 2015.

Haka kuma kwamitin ya ba shugaba Buhari shawarar cewa ya nada sabon shugaban hukumar EFCC ba tare da bata lokaci ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *