Hukumar hana sha da fataucin moiyagun kwayoyi NDLEA, ta ce ta na tunanin sakin sabuwar dokar da za ta tilasta yi wa ‘yan mata gwajin miyagun kwayoyi kafin su yi aure.

Shugaban hukumar Mohammed Mustapha Abdalla ya bayyana haka, yayin kona miyagun kwayoyin da su ka kwace a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Ya ce akwai bukatar a fara gwajin miyagun kwayoyi a cikin jerin gwaje-gwajen da za a mika wa majami’u da masallatai kafin a daura aure.

An dai fara tunanin ne, sakamakon yadda ‘yan mata da matan aure ke tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin Nijeriya.

Ya ce kiyasin ‘yan kwanakin nan ya nuna cewa, yawan masu tu’ammali da miyagun kwayoyi ya na raguwa a cikin maza, amma ya na karuwa a cikin mata matasa da matan aure.

Mustapha Abdalla, ya ce hukumar NDLEA ta na tunanin fara hada kai da shugabannin addinai wajen maida gwajin miyagun kwayoyi ya zama dole a jerin gwaje-gwajen da za a mika sakamakon su kafina daura aure.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *