Rundunar Tsaro ta farin kaya ta DSS, ta ce masu fafutukar kafa kasar Biafra sun kashe jami’an su biyu a wata arangama da su ka yi a Jihar Enugu, yayin da kungiyar ta ce jami’an tsaron sun kashe mata mutane 21.

Kakakin rundunar tsaro ta DSS Peter Afunanya, ya ce ‘yan kungiyar IPOB sun kai wa motar jami’an su hari a Emene da ke Enugu, inda aka hallaka biyu.

A nata bangaren ta bakin kakakin ta Emma Powerful, kungiyar ta zargi jami’an tsaron da kashe mata mutane 21.

A wata Sanarwa da hukumar DSS ta fitar, ba ta ce an kashe wani dan kungiyar Biafra ba, kuma babu wata hanyar tabbatar da cewa an kashe mutane 21.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam na ciki da wajen Nijeriya, sun sha zargin jami’an tsaron Nijeriya da kisan ‘yan kungiyar ta IPOB.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *