Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum, ya ce dole gwamnati ta maida hankali wajen tsananta maida ‘yan gudun Hijira garuruwan su domin su cigaba da noma da kiwo da sauran sana’o’in da su ke yi, idan ba haka ba kuma za su cigaba da shiga kungiyar Boko Haram.

Yayin zantawar sa da manema labarai, Zulum ya ce gwamnati ta gaza wajen wadata ‘yan gudun hijira da abincin da za su ci su koshi a sansanonin su.

Ya ce bai taba zuwa wajen shugaban Kasa ya nemi a sauya ko a cire wani shugaban rundunar tsaro ba, amma ya nemi a gyara matsalolin da sonoji da sauran su ke fama da su.

A cewar sa, kungiyar Boko Haram na ribatar mutane domin su shiga cikin ta, kuma hakan abin tsaro ne, don haka idan har jama’ar da ke sansanonin ‘yan gudun hijra ba su samu abin da su ke so ba dole ne su shiga kungiyar Boko Haram.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *