Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty Intanertional, ta ce ‘yan bindiga sun kashe kimanin mutane dubu 1 da 126 a jihohin arewacin Nijeriya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.

A wani rahoton da ƙungiyar ta fitar, ta ce an raba ɗaruruwan mutane da gidajen su a jihohin Kaduna da Neja da Katsina da Filato da Taraba da kuma Zamfara.

Amnesty, ta ce tun daga shekara ta 2016 ta ke bibiyar matsalar ‘yan bindiga da rikicin makiyaya da manoma.

Ta ce hukumomin Nijeriya sun bar mutanen karkara a hannun ‘yan bindiga, lamarin da ke ƙara haifar da tsoro da fargaba a kan wadatuwar abinci a yankunan karkara.

Hukumomin Nijeriya da su ka musanta rahoton Amnesty, har yanzu ba su fitar da martani game da rahoton ƙungiyar ba.

Amnesty ta ce ta tattara bayanan rahoton ta ne bayan tattaunawa da mutane a jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Filato da Sokoto da Taraba da kuma Zamfara, waɗanda su ka shaida mata cewa an bar su su na rayuwa cikin fargaba da tsoron hare-hare da garkuwa da su yayin da matsalar tsaro ke ƙara ƙamari a yankunan karkara.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *