Ministan harkokin yankin Neja Delta Sanata Godswill Akpabio, ya ce hukumar NDDC ta zama tamkar na’urar ATM, inda  ‘yan siyasar yankin ke tatsar kudaden da su ke gudanar da yakin neman zabe.

Godswill Akpabio ya bayyana haka ne, yayin karbar bakuncin tawagar kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya IPMAN a Abuja, inda ya ce matsalolin rashawa da almundahana sun dade da yi wa hukumar NDDC katutu taswon shekaru 19 kafin ya zama ministan ma’aikatar.

Ya ce kamata ya yi majalisun dokoki su fadada binciken da su ke a kan laifuffukan sace kudaden hukumar tsawon shekaru 19, maimakon zarge-zargen almundahanar kudaden daga watan Fabarairu zuwa Yuli na shekara ta 2020.

Ministan ya kara da cewa, Naira tiriliyan 5 gwamnati ta ba hukumar NDDC a tsawon shekaru 19 ba tare da an aiwatar da ayyukan da aka tsara yi da su  ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *