Mutane biyu sun rasa ransu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin ‘yan ƙungiyar dake fafutukar kafa kasar Biafra IPOB da ‘yan sanda.

Wasu majiyoyi sun ce arangamar ta faru ne ranar Lahadin nan kuma an jikkata wasu dama daga cikin ‘ya’yan ƙungiyar da suka fito zanga-zanga.

Jami’an ‘yan sandan sun kuma kama wasu da yawa daga cikin ‘yan kungiyar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Ahmad Abdurraham bai amsa saƙon tes da Punch ta aika masa ba har zuwa lokacin wannan rahoton.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *