‘Yan bindiga sun kashe wani kurtun ɗan sanda a ofishin ‘yan sanda na Ikolaba da ke birnin Ibadan na Jihar Oyo kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin da maharan su ka buɗe wuta a kan ofishin bayan sun shiga cikin farfajiyar ginin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni sun fara gudanar da bincike.

Ya ce sun samu labarin harin, amma bai samu ƙarin bayani game da ɗan sandan da aka ce an kashe ba, sai dai sun tura jami’an tsaro yankin kuma da zarar sun samu ƙarin bayani za su sanar da manema labarai.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *