Dakarun sojin Nijeriya na rundunar ‘Operation Sahel Sanity,’ sun kashe mahara uku tare da kama wasu maharan 10, sannan sun ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara.

Mataimakin Shugaban sashen yada labarai na rundunar Benard Onyeuko ya Sanar da haka a Katsina, inda ya ce a ranar 16 ga watan Agusta dakarun sun gudanar da bincike a wata maboyar maharan da ke dajin Dumburum.

Onyeuko, ya ce dakarun sun kutsa cikin dajin da ke kewaye da jihohin Katsina da Zamfara tun daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Agusta.

Idan dai ba a manta ba, Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Tsaron Nijeriya John Enenche, ya ce dakarun soji na ‘Operation Lafiya Dole’ sun kashe ‘yan ta’adda da dama a kauyen Tashar-Kare da ke jihar Neja.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *