Shugabannin kungiyar kungiyar rainon tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS sun kai ziyara Mali domin ganawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita dan ganin an gaggauta maido da mulki fararen hular kasar.

Tawagar da ke karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta gana da tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita dake tsare a barkin soji da kuma shugabannin sojin.

Shugabannin ECOWAS sun ki amincewa da juyin mulkin, duk da ya samu goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU da kuma kasashen Faransa da Amurka.

‘Yan adawar Mali sun amince da juyin mulkin kamar yadda suka bayyana a taron gangamin da suka gudanar jiya a Bamako, inda suka bayyana aniyar su ta aiki tare da sojojin domin mayar da Mali turbar dimokiradiya.

Tuni kungiyar ECOWAS ta hannu shugaban ta Mahamadou Issofou ta sanar da takunkumi kan kasar ta Mali da kuma wasu daga cikin jami’an sojin da suka karbe iko.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *