Majalisar shari’ar addinin musulunci ta Nijeriya, ta bayyana matakin da kungiyar lauyoyi ta kasa ta dauka na soke gayyatar gwamna El-Rufa’i zuwa taron da ta shirya a matsayin abin takaici.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren majalisar Nafi’u Baba Ahmed ya raba wa manema labarai, majalisar ta ce abin da kungiyar lauyoyin ta yi ya zubar mata da kima a idon al’ummomin Nijeriya.

Ta ce bai dace kungiyar ta rika nuna bangaranci ko son kai a cikin al’amurran ta ba, musamman ganin yadda lauyoyin su ka yi amfani da rikicin kudancin Kaduna domin raba kan jama’a.

Majalisar shari’ar ta cigaba da cewa, rikicin manoma da makiya ba sabon abu ne a Nijeriya ba, don haka kamata ya yi kungiyar lauyoyin ta hada hannu da gwamnatin wajen lalubo hanyayoyin magance matsalar, ba su rika amfani da siyasa ko bambancin addini domin cimma muradin wasu tsiraru ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *