Majalisar Dattawa ta rubuta wa Hukumar Hada-hadar Cinikin Mai ta Kasa DPR wasikar neman sanin yadda aka yi da cinikin fetur na naira Tiriliyan 2 da biliyan 400 a shekara ta 2019.

Rahotanni sun ce, majalisar ta nuna damuwa ne, ganin yadda alkaluma su ka nuna cewa naira biliyan 44 da rabi kadai hukumar DPR ta zuba cikin Asusun Ajiyar Cinikin Fetur maimakon naira tiriliyan 2 da biliyan 400 a shekara ta 2019.

Majalisar ta nemi sanin yadda aka yi da kudaden, da kuma dalilin da ya sa ba a zuba su a asusun da doka ta ce a rika zubawa ba.

Hakan kuwa ya taso ne, bayan shugabannin hukumomin tara kudaden shiga daban-daban sun ki bayyana a gaban Kwamitin Kasafi da Tsare-tsare na Majalisar, domin su yi bayanin kintacen kudaden shigar da su ka ce za su samu a cikin kasafin shekara ta 2021.

Shugaban kwamitin Solomon Adeola ne ya fara tada balli, a lokacin da ya nemi sanin adadin kudaden shigar da Hukumar DPR ta tara a shekara ta 2019.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *