Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya CAN, ta ce sabuwar dokar maida kamfanoni da kungiyoyi a karkashin kulawa da sa-idon hukumar kula da kamfanoni da kuma kungiyoyi ta kasa CAC, ba ta dace ba kuma za ta bijire mata.

Shugaba Muhammdu Buhari dai ya sa ma dokar hannu ne a ranar 7 Ga watan Agusta, wadda ta tilasta wa kamfanoni da kungiyoyin addinai yin rajista da hukumar CAC kuma za su kasance a karkashin sa-idon wani Minista.

Haka kuma, dokar ta karfafa cewa, gwamnati na da ikon cire shugabannin kwamitin amintattu na wata Kungiyar addini idan akwai rikici ko tankiya a cikin shugabancin kungiyar.

Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya ta ce wannan doka karfa-karfa ce kuma ba abin yarda ba ce, sannan ta ce dokar tamkar yi wa Ubangiji shisshigi ne.

Kungiyar Kiristocin ta bayyana haka ne, a cikin wata sanarwa da Kakakin ta Adebayo Olajide ya raba wa manema labarai.

CAN ya kara da cewa kungiyar addini na gudanar da hidimar daukaka kalmar Ubangiji da kudaden ta, tare da ayyukan kusantuwa ga Allah abin bauta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *