Ministar Ma’aikatar Agaji da Ci-gaban Al’umma Sadiya Umar Farouq, ta ce shirin N-Power ya azurta matasan da su ka ci gajiyar shirin ta hanyar maida mutane dubu 109 da 823 ‘yan kasuwa.

Sadiya Farouq ta bayyana haka ne, a wajen taron da aka shirya na cika shekara guda da kafa ma’aikatar ta, inda ta ce ƙididdigar ƙarshe ta nuna kusan matasa dubu 109 da 823 na Rukunin farko da na biyu sun kafa harkokin kasuwanci a unguwannin su.

Ta ce sun samu nasarar cire mutane dubu 500 na Rukunin farko da na biyu daga shirin, sannan sun rufe karɓar rajistar Rukuni na uku, inda mutane miliyan 5 da dubu 42 da 1 su ka nema.

Ministar ta kara da cewa, yayin da su ke ƙoƙarin fara tantancewa, ma’aikatar su za ta tabbatar cewa an yi adalci domin ganin waɗanda su ka cancanta kawai za a ɗauka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *