Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sassuta dokar hana fita a ƙananan hukumomin Zangon Kataf da Kauru.

A cikin wata Sanarwa da Kwamishinan Tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ya ce daga yanzu dokar za ta riƙa aiki ne daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe.

Ya ce yayin da su ke ƙoƙarin daƙile salwantar rayukan al’umma da tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin Atyap da Fulani da Hausawa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da shawarar sassauta dokar hana fita.

Idan dai ba a manta ba, tun ranar 11 ga watan Yuni na shekara ta 2020 ne aka sa dokar hana fita ba dare ba rana bayan wani rikicin ƙabilanci tsakanin Hausawa da ‘yan ƙabilar Atyap a kan wata gona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *