Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Abubakar, ya dora laifin tsadar kayan abinci da ‘yan Nijeriya ke kuka da ita a kan gwamnatin da ta gabata.

Ya ce an rika tafiyar da mulki a makance wajen maida hankali ga shigo da kayan abinci iri daban-daban a Nijeriya, ba tare da yin la’akari da noma irin sa ko madadin sa a kasar nan ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne, a wajen taron kaddamar da wasu ayyuka na Shiyyoyin Nijeriya shida da Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami ya yi a Abuja.

Ya ce ya zama dole a fuskanci matsalar tsadar kayan abinci, tunda sun gaji gwamnatin da a lokacin ta ana saida gangar danyen mai dala 100 har zuwa 120, amma ta kasa kirkiro hanyoyin noma abincin da za a ci a kasar nan ta kuma hana shigo da shi daga waje.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatin da ta gabata ba ta tanadi wani nagartaccen tsarin wadatar da abinci ko hana shigo da kayayyaki daga waje ba.

Sai dai jama’a na ta korafin cewa, rufe Kan iyakokin Nijeriya ya kara haifar da tsadar kayan abinci da kayan masarufi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *