Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya jagoranci jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi domin ƙona wasu ƙwayoyin magani da hukumar ta kama.

Yayin taron wanda shugaban hukumar NDLEA Kanar Mustapha Abdallah ya shirya, an ƙona Ton 20 ko kuma kilogiram dubu 20 na ƙwayoyin da hukumar ta kama a samame daban-daban.

A cikin wata Sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce bikin ya gudana ne a Muna da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Gamboru ta Jihar Borno.

Daga Cikin manyan baƙin da su ka halarci bikin har da Mai Alfarma Shehun Borno, da manyan jami’an rundunar sojin Nijeriya da kwamishinoni da shugabannin addinai.

A jawabin sa, Gwamna Zulum ya ce ya kaɗu da yawan ƙwayoyin da hukumar NDLEA ta ƙwace, sannan ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da taimaka wa hukumar wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *