Ƙungiyar mabiya akidar shi’a bangaren sheikh Ibrahim El-Zakzakky, ta yaba da matakin da ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya ta ɗauka na janye gayyatar da ta yi gwamnan Nasir El Rufa’i domin ya yi jawabi a babban taron da za ta gudanar a wannan watan.

Idan dai ba a manta ba, Ƙungiyar Lauyoyin ta janye gayyatar da ta yi wa El-Rufa’i ne ranar Alhamis da ta gabata, bayan zanga-zangar da wasu lauyoyi su ka yi a kan gayyatar.

A wani saƙo da Ƙungiyar Lauyoyin ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce ta shaida wa gwamnan matakin da ta ɗauka na janye goron gayyatar sa ne, bisa koken wasu ‘ya’yan ta da ke zargin gwamnan da gazawa wajen shawo kan rikicin Kudancin jihar Kaduna da kuma take haƙƙn bil adama.

A cikin wata sanarwa da kakakin ta Ibrahim Musa ya raba wa manem alabarai, kungiyar ‘yan shi’a ta ce gwamnan bai cancanci halartar taron ba.

Gwamnatin jihar Kaduna da ta wallafa a shafin twitter amincewar da El Rufa’i yi wa goron gayyatar, bayan ƙungiyar lauyoyin ta janye gayyatar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *