Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada tsohon tauraron kwallon kafa Daniel Amokachi a matsayin mai taimaka ma shi a kan harkokin wasanni.

Ministan wasannin Sunday Dare ya sanar da nadin, sakamakon wasikar da Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya rubuta, wadda ta bayyana amincewar shugaba Buhari na ba Amokachi mukamin.

Wasikar da aka aike wa Amokachi, ta ce shugaba Buhari ya na farin cikin sanar da shi nadin da aka yi ma shi daga ranar 11 ga watan Agusta.

Daniel Amokachi dai ya na daga cikin fitattun ‘yan kwallon kafar da su ka daga darajar Nijeriya wajen lashe mata kofin Afirka da Olympics, yayin da ya yi wa kungiyar Everton ta Ingila da Club Brugge ta Belgium da kuma Besiktas ta Turkiya wasa.

Sau Amokachi ya na lashe kyautar dan wasan Afirka da ya fi fice saboda kwarewar sa, yayin da ya taka rawa wajen kai Nijeriya gasar cin kofin duniya na farko a Amurka da Faransa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *