Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya reshen Jihar Jigawa, ta yi barazanar fasa halartar taron gangamin yanar gizon da uwar kungiyar ta shirya sakamakon janye gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i.

A cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar Garba Abubakar ya fitar, Kungiyar ta ce zarge-zargen da ake yi wa El-Rufa’i shirme ne kawai saboda ba a bashi damar kare kan sa ba.

Garba Abubakar, ya ce wani bangare na kasar nan ba za su raina masu hankali ba, saboda dukkan su su na da fahimtar doka.

Don haka ya ce su na kira ga shugaban kungiyar na kasa Paul Usor ya janye wannan shawara da gaugawa, idan kuma ba haka ba kungiyar Lauyoyi reshen jihar Jigawa ba za ta halarci taron gangamin ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *