Ministar Agaji da Jinkai Sadiya Farouq, ta ce gwamnatin tarayya ta tallafa wa ‘yan gudun hijira dubu 5 da 576 da ke zama a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Wuse a Abuja.

Sadiya ta ce gwamnati ta yi haka ne, a daidai lokacin da duniya ke tunawa da ranar bada Agaji da Jinkai da kuma cikar shekara daya da kafa ma’aikatar samar da Agaji da jinkai a Nijeriya.

Minista ta kara da cewa, gwamnati ta raba kayan abincin da su ka hada da buhunan na shinkafa 80, da buhunan wake 15 da jarkoki 25 na man gyada, da barguna 500 da turamen zannuwa 100.

Jami’in sansanin Jeoffery Bitrus, ya mika godiyar sa a madadin mazauna sansanin ga minista bisa wannan tallafi da su ka samu, ya na mai karin haske da yin kira ga gwamnati ta gina asibiti a sansanin domin kiwon lafiyar mazauna wurin.

Shugaban kungiyar mata a sansanin Hafsat Ahmad, ta roki gwamnati ta sama masu hanyar da za su rika koyon sana’a don su iya rike kan su su ma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *