Yara biyu sun samu rauni, yayin da wani abin fashewa na yakin basasar Nijeriya a shekara ta 1967 zuwa 1920 ya fashe a garin Eziorsu Ugwuta da ke jihar Imo.

An dai samu fashewar abin ne a ranar Talatar da ta gabata, yayin da yaran ‘yan tsakanin shekaru 10 zuwa 16 su ka yi amfani da shi wajen kokarin kunna wuta domin gasa rogo kusa da harabar gidan su.

Mahaifin yaran Goddey Uzi, ya ce ya abubuwan su na kusa da gidan sa, kuma ya dade ya na amfani da su domin amfanin gida.

Garin Eziorsu dai ya sha fama da fashewar abubuwa tsawon shekaru bayan kammala yakin Biafra a shekara ta 1970.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *