Rundunar ‘yan sanda ta jihar katsina, ta kama wani jami’in hukuma kula da shige da fice ta Nijeriya mai mukamin Sufeta tare wasu mutane biyar da shanun sata 164.

Jami’in mai suna Abubakar Shafiu ya bayyana wa manema labarai cewa, wadanda aka kama su tare ‘yan’uwan sa ne da ke zaune a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Shafiu wanda ya ce ya samu hutu a wajen aiki ne, yanzu kuma ya fitar da motocin shanu daga Zamfara kafin a kama su, sai dai ya musanta zargin cewa shanun sata ne, inda ya ce kawai masu shanun ne ke kokarin kai su Potiskum da Buni Yadi a jihar Yobe saboda hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da rahoton, ya ce an kama mutanen ne a Jibiya, bayan wasu bayanan sirrin da jami’a ‘yan sanda da na kwastam su ka samu cewa ana tafiyar da shanun da ake zargin na sata ne kuma Shafi’u ya na raka su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *