Wasu bakin haure uku da ke kawo wa ‘yan ta’adda makamai a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya sun shiga hannu, bayan jami’an hukumar soji da ke kula da shiyyar jihar Sokoto sun kama su.

Mai magana da yawun helkwatar tsaro ta kasa Manjo Janar John Enenche, ya ce masu laifin, wadanda su ka yi shiga irin ta ‘yan Nijeriya, an kama su da makamai a kauyen Dantudu da ke cikin karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Makaman da aka samu a wajen su kuwa sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda shida, da harsashi guda dubu 2 da 415, wadanda duk aka samu a cikin abubuwan hawan da su ke amfani da su wajen tafiye-tafiye.

Rahotanni sun ce, tuni wadanda ake zargin su na hannun jami’an tsaron ana ci-gaba da bincike a kan su, inda daga baya za a mika su ga hukumar da ta dace domin yi masu hukunci.

Enenche ya kara da cewa, hakan ya na nuni da cewa, wasu matsalolin tsaron da ke faruwa a Nijeriya akwai sa hannun mutanen da ba ‘yan kasa ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *