Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da sabunta naɗin Mista Joseph Chiedu Ugbo a matsayin shugaban hukumar samar da lantarki ta yankin Neja Delta.

Bayanin ya na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa mataimakin shugaban ƙasa ta fuskar yada labarai Laolu Akande ya fitar.

Sanarwar, ta kuma ambato haɗin Mr Babayo Shehu da Ifeoluwa Oyedele a matsayin manyan daraktocin hukumar na wa’adin shekaru hudu, kuma sabunta naɗin zai fara aiki ne daga ranar 25 ga watan Agusta na shekara ta 2020.

Ya ce an kuma amince da nadin wasu ƙarin manyan daraktoci uku a hukumar, domin inganta aiki da fadada aikin kamfanin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *