Babban sufeton ‘Yan sandan Najeriya Mohammad Adamu, ya ce matsalolin ta’addancin da ake fama dasu a yankin arewa maso yammacin Najeriya na da alaka da wasu kasashe.

Adamu ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na musamman da aka shirya kan zaman lafiya da tsaro a karamar hukumar Zuru dake jihar Kebbi.

Shugaban ‘yan sandan ya ce ya kai ziyarar ce tare da wasu kwararru kan tattara bayanan sirri da sauran su.

Adamu ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da bada gudunmawa wajen yaki da ayyukan ta’addanci wanda a cewarsa ba abu ne na mutum guda ba matukar ana sa a kai ga nasara.

Ya ce ba jami’an tsaro bayanan sirri, da kuma gudunmawa wajen fitar da masu laifi dake cikin su zai taimaka wajen magance matsalar baki daya a yankin dama Najeriya baki daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *