Gwamnatin tarayya ta ce bullar cutar korona a fadin duniya kalubale ne babba ga shirin cimma muradun karni.

Mai ba shugaban kasa shawara kan shirin cimma muradun karni Adejoke Orelope-Adefulire, ta bayyana haka a taron cimma muradun karni da aka gudanar ta fasahar zamani.

Da take jawabi a taron Orelope-Adefulire, ta ce illar da annobar korona ta yiwa tattalin arziki ya shafi Najeriya sosai, musamman duba da cewa kasa ce da ta dogara da bangaren man fetur.

Orelope-Adefulire, wacce ta samu wakilcin Bala Yusuf, ta ce cutar ta korona ta fito da irin shirin da kasashen da suka ci gaba suka yiwa bangaren lafiya. Ta ce samar da kudaden shirin na raya muradun karni ba yana nufin harhada jari bane na aikace-aikace da shirye-shirye.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *