Gwamnatin tarayya ta ce gwamnatocin jihohi basa yin abin da ya kamata wajen kubutar da rayuka da dukiyoyin al’umma sanadiyyar ambaliyar ruwa.

Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya da hukumar NIHSA suka bayyana haka a wajen wani taro na musamman da aka shirya domin magance matsalar ambaliyar ruwa.

Taron bitar da ya samu goyon bayan kungiyar tarayyar Afirka da kungiyar tarayyar Turai ya maida hankali wajen zakulo sabbin dabaru da za a rika amfani dasu wajen magance matsalar.

Shugaban hukumar NIHSA, Clement Nze, ya ce akwai bukatar gwamnatoci su tashi tsaye wajen amfani da bayanai da shirye-shirye da aka samar domin kubutar da al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *