‘Yan bindiga sun kashe mutane goma sha daya tare da jikkata wasu da dama a wani sabon harin da su ka kai kauyen Unguwar Gankon da ke Zangon Kataf da kauyen Maro a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Harin dai, na zuwa ne kasa da mako guda bayan helkwatar tsaro ta tura dakaru na musamman daga rundunar sojin sama da na kasa zuwa kudancin Kaduna domin shawo kan matsalar kashe-kashe a yankin.

Duk da hukumomin ‘yan sanda ba su tabbatar da lamarin ba, amma Elias Manza ya shaida wa manema labarai cewa harin na ramuwar gayya ne daga wasu mahara su ka kai a daren ranar Talatar da ta gabata.

Elias Manza ya kara da cewa, dakarun sojin kasa da sama na musamman sun isa wasu daga cikin garuruwan a kokarin kare mazauna yankin daga harin ‘yan bindiga.

Shugaban karamar hukumar Kajuru Cafra Caino ya tabbatar da cewa, ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu da ke tafiya a motar kasuwa a kauyen Maro, wani da ke tsakanin kananan hukumomin Kajuru da Kachia.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *