Ƙungiyar ta’addanci ta IS, ta ce ta kashe sojojin Nijeriya bakwai a garin Kukawa da ke jihar Borno, yayin da wasu rahotanni ke cewa mayakan sun kuma yi garkuwa da mutane da dama a garin.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar IS ta ce mayakan ta sun kai hari sansanin Soji, inda su ka yi artabu da su tare da ikirarin kashe mutane bakwai baya ga raunata wasu, sannan ta kwace motocin yaki da makaman sojoji.

Rahotanni daga jihar Borno na cewa, mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari garin Kukawa tare da hana mutane fita daga ciki.

Har yanzu dai rundunar sojin Nijeriya ba ta ce komai a kan harin ba, wanda ya ke zuwa kwanaki kaɗan bayan ɗaruruwan ‘yan gudun hijira sun koma garin da zama.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *