Tawagar wakilai ta shugabannin ƙasashen yammacin Afirka za su kai ziyara ƙasar Mali.

Shugabannin ƙasashen Nijar da Senegal da Ghana da Ivory Coast ne ake sa ran za su wakilci sauran shugabannin kasashen na Afrika ta yamma.

A baya, shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS sun yi yunƙurin sasanta rikici a lokuta daban-daban ciki har da yunƙurin kafa gwamnatin haɗaka.

Sai dai ‘yan adawa sun yi watsi da yunƙurin kuma suka haƙiƙance cewa sai Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ya sauka daga mulki.

Da yammacin Talata ne sojoji suka tilasta wa Keita sauka daga muƙamin nasa sannan suka hau karagar mulki tare da yin alƙawarin shirya sabon zaɓe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *