Rundunar soji da ta hamɓarar da Shugaban Mali, Ibrahim Boubacar Keïta ta kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kafin gudanar da sabon zaɓe a ƙasar.

Wannan ya biyo bayan sauka daga kan karagar mulki da shugaban na Mali ya yi.

Rundunar sojin ta kuma bada umarnin rufe iyakokin ƙasar tare da sanya dokar hana fita da dare.

Wata sanarwa da mataimakin shugaban ma’aikatan sojojin sama na ƙasar ya fitar ta ce daga yau, 19 ga watan Agusta, an rufe dukkanin iyakoki na sama da na ƙasa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *