Mazauna garuruwan da ke kan iyakokin Nijeriya sun ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba shekara guda bayan gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin tudu.

A watan Agusta na shekara ta 2019 ne, gwamnatin Nijeriya ta rufe iyakokin ta, da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri tare da bunƙasa tattalin arziki.

Hukumar yaki da fasa-ƙwauri da ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da dokar rufe iyakokin, ta bugi ƙirji game da irin nasarorin da Nijeriya ta samu ta fuskoki daban-daban.

Kakakin hukumar kwastam na ƙasa Joseph Attah ya shaida wa manema labarai cewa, in da Nijeriya ba ta ɗauki matakin rufe iyakokin ba da ta fuskanci matsala ta ɓangaren abinci bayan ɓullar annobar korona.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *