Hukumar kididdig ta kasa NBS, ta sanar da samun karuwar marasa aikin yi daga kashi 23.1 zuwa kashi 27.1 a watanni 6 na farkon shekara ta 2020.

Bayanan da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yanzu haka Kano ke matsayin ta biyu a jerin jihohin da ke da yawan marasa aiki a Nijeriya, wadanda galibin shekarun su sun fara daga 15 zuwa 60.

Alkaluman hukumar sun nuna cewa, jihar Kano na da jimillar mutane miliyan 1 da dubu dari 4 da 20, kuma galibin su matasa ne da ba su da aikin yi.

Yanzu haka dai Nijeriyar ta na da alkaluman mutane miliyan 21 da dubu 764 da 617 da ba su da aiki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *