Jami’an ‘yan sanda sun ceto iyalan dan majalisar dokoki ta jihar Bauchi da ‘yan bindiga su ka yi wa kisan gilla Musa Mante Baraza.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnan jihar Bauchi Dakta Ladan Salihu ya sanar da haka a shafin sa na Twitter, inda ya ce an sako matan dan majalisar da aka kashe kwanaki hudu da su ka gabata.

Tuni dai gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya ba likitoci da jami’an tsaro umarnin ba iyalan mamacin kulawa da tsaro.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, inda Kakakin rundunar DSP Ahmed Wakili ya sanar da manema labarai cewa, tabbas jami’an ‘yan sanda sun ceto wadanda aka sace bayan wasu bayanan sirri da su ka samu.

Ahmed Wakili ya kara da cewa, sun samo mutanen ne a wani kauye mai suna Bashi da ke cikin karamar hukumar da aka sace su, sai dai ya duk da ceto wadanda aka sacen da su ka yi har yanzu ba a samo wadanda ake zargin ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *