Rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo, ta kama mutane 15 da ake zargin sun kai wa gwamnan jihar Hope Uzodinma hari a ranar Litnin da ta gabata.

Harin dai ya auku ne, yayin da gwamnan ke kan hanyar zuwa wajen kaddamar da wani sabon barikin Soji da gwamnatin jihar ta gina.

‘Yan bindigar rike da bindigogi da adduna, sun yi ikirarin cewa su ma’aikatan hukumar ci-gaban garuruwa masu arzikin man fetur a jihar ne, kuma su na zanga-zanga bisa rashin biyan su albashi.

Kwamishanan ‘yan sanda na jihar Isaac Akinmoyede, ya ce ‘yan bindigan sun ce su ma’aikatan hukumar ne kuma an hana su albashi tsawon watanni uku.

Ya ce an kama masu zanga-zangar da wata karamar bindiga daya, da adduna biyu, da takunkumin rufe fuska daya da kuma  sarka da kwado.

Akinmoyede, ya ce sun kai wa jerin motocin gwamnan hari da karamar bindiga da kuma adduna, sai dai bai yi sanadiyar mutuwar kowa ba, amma an fasa gilasan motocin gwamnan an kuma lalata motoci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *