Ministan Sufuri Rotimi Ameachi,  zai sake bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai domin yi masu bayani a kan bashin da Nijeriya ta karɓo daga kasar China da sunan gina layin dogo.

A ranar Litinin da ta gabata ne, Amaechi ya fara bayyana a gaban kwamitin, inda su ka tafka muhawara tare da jefa wa juna zafafan kalamai game da sharuɗɗan da Nijeriya ta yarda da su yayin ƙulla yarjejeniyar da kasar China.

‘Yan majalisar sun zargi ministan da amincewa da sharuɗɗan da China ta gindaya tun kafin sanya hannu a kan yarjejeniyar.

Amaechi ya buƙaci ‘yan majalisar su dakatar da bincike a kan bashin kuɗi sama da naira biliyan 153 da China ta bada a shekara ta 2018, ya na mai cewa binciken zai sa China ta jinkirta ba da wani bashin nan gaba.

Yanzu haka dai China ta na bin Nijeriya bashin Dala biliyan 3 da miliyan 100, yayin da ‘yan Nijeriya ke bayyana damuwa game da sharuɗɗan yarjejeniyar, waɗanda su ka ce ana ƙoƙarin saida ‘yancin Nijeriya ne ga kasar China.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *