Cibiyar kula da masana’antu, ma’adanai, zuba jari da harkokin noma ta Najeriya ta bukaci a kara karfafa dangantaka a tsakanin Najeriya da kasar Indonesia musamman a bangaren ci gaban noma. 

Shugaban cibiyar ta kasa Saratu Iya, ta bukaci hakan a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Legas.

An fitar da sanarwar ce bayan ganawar da aka yi ta fasahar zamani da ‘yan kasuwar Najeriya da na kasar Indonesia akalla 70 suka halarta.

A cewarta karfafa dangantakar musamman a bangaren kasuwancin kayayyakin gona zai kara bunkasa harkokin noman a Najeriya yadda ake bukata.

Shima a nasa jawabin jakadan kasar Indonesia a Najeriya Usra Hendra Harahap, ya ce karfafa dangantakar musamman a bangaren kasuwancin zai taimakawa kasashen biyu ta bangarori masu zaman kansu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *