Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce tana goyon bayan ba bangaren shari’a cin gashin kai.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Feyemi, ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin zababben shugaban kungiyar Lauyoyi ta Najeriya Olumide Akpata a ofishinsa dake Ado Ekiti.

Fayemi ya ce ingantuwar bangaren shari’a shine kashin bayan kowanne demokradiyya, a don haka akwai bukatar bukatar da gyare-gyare domin tabbatar da ci gaban bangaren.

Ya kara da cewa shi da kansa ya jagoranci tawagar gwamnoni inda suka gana da shugaban Alkalan Najeriya, Mai shari’a Ibrahim Tanko Mohammad da shugabar kotun daukaka kara Monica Dongban Mensem domin tattauna yadda za a ba bangaren shari’a damar cin gashin kai a jihohi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *