Gwamnatin tarayya ta ce za a maido da sufurin jiragen sama na ƙasashen ketare daga ranar 29 ga wannan watan na Augusta da muke ciki.

Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya wallafa haka a shafinsa na twitter

Ya ce za a fara jigilar ne a Legas da Abuja kamar yadda aka fara da dawo da jigilar jirage na cikin gida.

Ministan ya kara da cewa za a maido da sufurin jiragen ne ta hanyar amfani da matakan kariya da hukumomin lafiya na duniya suka amince dasu.

Ya kara da cewa fasinjojin za su rika yin gwajin cutar korona kwanaki kadan kafin tashin su zuwa wata kasa, sannan su sake yin wani gwajin kwanaki 8 bayan saukarsu a kasar da suka je.

Ya ce fasinjojin su da kansu za su rika biyan kudin gwajin cutar da za a rika musu na cikin gida.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *