Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Karatun Sakandare Ta Afrika Ta Yamma WAEC, ta gargaɗi ɗalibai cewa satar amsar Jarrabawar Lissafi da ke yawo a shafukan sada zumunta ta bogi ce.

Ta masu zamba ne su ka samar da irin waɗannan takardun jabun, inda su ke so su yi amfani da su doimn karɓar kuɗaɗe daga hannun mutane.

A ranar Litinin din nan ne, ɗaliban ajin ƙarshe na sakandare a faɗin Nijeriya ke soma rubuta jarrabawar su ta kammala karatu, bayan an samu jinkirin watanni saboda annobar cutar korona.

Sama da dalibai miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne ake sa ran za su ɗauki tsawon makonni su na rubuta jarrabawar ta WAEC.

Hukumar ta kara da cewa, duk wani ɗalibin da ya karɓi takardun jabun zai sha mamaki, yayin da ya shiga ɗakin jarrabawa ya ga ta sha bamban da wadda za a ba shi.

Mai magana da yawun Hukumar Demianus Ojijeogu, ya ce ɗaliban Ghana ba su zana jarrabawar Lissafi ta wannan shekarar ba kamar yadda mutane ke faɗa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *