Alƙalumman Hukumar Ƙididdiga ta kasa NBS sun nuna cewa, Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ƙaru zuwa kashi 12.82 cikin 100 a watan Yuli.

Wani rahoton hukumar  a kan farashin kayan abinci na daban ya nuna tashin farashin kayayyakin abinci zuwa kashi 15.48 cikin 100 a watan Yuli, wanda ya fi na watan Yuni na kashi 15.18 cikin 100.

Haka kuma, alƙaluman na shekara sun ƙaru ne a kan kashi 12.56 cikin 100 da aka samu a watan Yuni.

Nijeriya dai ta na fama da rikicin tattalin arziki da faɗuwar farashin mai ta haifar sakamakon annobar korona da kuma karyewar darajar Naira.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *