Gwamantin tarayya, ta ce za ta ɗauki matakin gaugawa game da wani bidiyo da ya ɓulla a shafukan sada zumunta da aka ce ‘yan Nijeriya ne ake wulaƙantawa a kasar Ghana.

Bidiyon ya nuna jami’an tsaro su na kulle shagunan ‘yan kasuwar ƙasashen waje, waɗanda akasarin su ‘yan Nijeriya ne.

Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama ya bayyana haka, inda ya ce ba su ji daɗin abin da su ka gani ba.

Ya ce Gwamnatin Nijeriya ba ta ji daɗi game da bidiyon da ya nuna yadda ake rufe shagunan ‘yan Nijeriya a kasar Ghana ba, don haka ya ce za su ɗauki matakan gaugawa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *