Jami’an gwamnatin kasar Kamaru sun bayyana cewa sun gano wani abun fashewa a kwali da ya kunshi takardun wasu malaman makarantu da aka dauka aiki.

Sun ce sun gano abin fashewar ne a lokacin da yake kara a wani ofishin da ke ma’aikatar.

Jim kadan bayan gano kayan aka kira jami’an tsaro na ‘yan sanda suka fitar da kunshin da ake tunanin bom ne.

Bayan binciken da aka yi an gano cewa wani abin fashewa ne da aka yi niyyar tadawa a cikin ginin ma’aikatar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *