Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin binciken aikin wani titi mai tsawon kilomita biyar da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bada, wanda ya ratsa kananan hukumomi 44 na jihar.

Haka kuma, gwamnatin ta amince da dakile kwangilar miliyoyin naira da ta bada a Dawakin Tofa, wanda ta ba kamfanin Messrs CCECC Nigeria Limited a kan Naira biliyan 651 da miliyan  844 da dubu 966 da 51.

An bada kwangilar ne a shekara ta 2012, amma an tsaya da aikin bayan an kai rabi, lamarin da ya janyo matsi da tsanani a yankin.

Kwamishinan yada labarai na jihar Muhammad Garba ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya ce matakin ya na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na dubawa da kammalawa ko kuma dakatar da duk wata kwangila.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *