Hukumar kula da harkokin tashoshin jiragen sama ta kasa FAAN, ta gargadi fasinjojin da ke zuwa Nijeriya su guji ba ma’aikatan ta cin hanci da rashawa.

FAAN ta yi zargin cewa, wasu jami’an ta da ke Abuja su na karbar kudade daga hannun masu zuwa Nijeriya domin gudun a yi masu gwajin cutar COVID-19 da sauran bincike.

Hukumar ta bayyana haka ne, dangane da wani sako da ke zargin ma’aikatan ta a tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe da karbar Naira dubu 50 zuwa 100 domin tsallakar da mutum daga killacewa.

Shugabar sashen harkokin hukumar Mrs. Henrietta Yakubu, ta ce hukumar ta gargadi fasinjoji da cewa babu wani aiki da za a yi masu da za su biya kudi.

Hukumar ta kuma yi nuni da cewa, duk fasinjojin da za su shigo Nijeriya sai an yi masu gwajin COVID-19 kafin su bar tashar jirgin da su ke.

Don haka ta ce kada su biya jami’an ta kudi domin tsallake gwaji.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *