Gwamnatin tarayya ta nesanta kan ta daga gayyatar da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi wa Ghali Umar Na-Abba bisa zargin yin kalamai a kan Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Shugaban Ƙasa Garba Shehu ya fitar, ta ce bayanan da su ka samu na farko-farko sun nuna cewa, gayyatar da aka yi wa Ghali Na’Abba ba ta da alaƙa da maganganun da ya yi.

Ana sa ran Ghali Umar Na’abba zai amsa gayyatar da hukumar DSS ta yi ma shi bayan wasu kalaman neman kawo sauyi a Nijeriya da ya yi a makon da ya gabata.

Ghali Umar Na’abba dai ya yi kalaman ne a ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna ‘National Consultative Front’ a Turance, inda ya ce Buhari ya na sane da alfanun samun ƙwaƙkwarar jam’iyyar adawa, ganin cewa shi ma daga nan ya fito.

Ya ce Shugaba Buhari ya taba cewa, burin sa shi ne ya gudanar da ingantaccen zaben da zai ba ‘yan ƙasa damar ɗora wanda su ke so a kan mulki, kuma duk wani abu akasin haka ba abin so ba ne.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *