An sake ceto wani mutum da mahaifinsa ya tsare shi tswon shekara 15 a jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘ya sandan Jihar Abdullahi Kiyawa ya ce an tsare Ibrahim Lawal ne mai shekara 33 tsawon shekaru 15 a wani ɗaki.

Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda aka fitar da mutumin daga wani ɗaki.

Abdullahi Kiyawa ya ce an ceto shi ne a unguwar Sheka da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Ya ƙara da cewa tuni aka kai mutumin asibiti sannan kuma sun fara bincike game da lamarin.

Wannan na zuwa ne kwana uku kacal bayan ceto wani mutumin da iyayensa suka tsare shi tsawon shekara uku.

Kazalika, a cikin makon da ya gabata ne aka kama iyayen wani yaro a Jihar Kebbi bayan sun ɗaure shi a turken dabbobi na tsawon lokaci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *