Gwamnatin tarayya ta ce basussukan da take karɓowa daga ƙasashen waje sun taimaka matuƙa wajen aiwatar da manyan ayyuka a faɗin ƙasar nan.

Ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar gani da ido dangane da aikin hanyar jirgin kasa da ake yi wacce ta taso daga Legas zuwa Ibadan zuwa Kano.

Ministan ya ce babu wata illa akan karbar rance muddin za’a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Lokacin da yake nashi jawabin Ministan sufuri Rotimi Amaechi, ya ce Najeriya na bukatar Dala Biliyan biyar da rabi wajen kammala aikin hanyar titin dogon, sannan ya yi kira ga majalisar tarayya da ta amince da shirin ƙarbo bashi dags ƙasar Chana domin tasirin da hakan yake dashi.

Ministan ya cigaba da cewar babu wata illa akan karbar rance muddin za’a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa.

Lokacin da yake nashi jawabin Ministan sufuri Rotimi Amaechi, yace Najeriya na bukatar Dala Biliyan biyar da rabi wajen kammala aikin hanyar titin dogon, sannan ya yi kira ga majalisar tarayya da ta amince da shirin ƙarbo bashi dags ƙasar Chana domin tasirin da hakan yake dashi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *